Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Abdullahi Muhammad Getso, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu tarbiyya da nagarta da su fito su shiga harkokin siyasa, domin gyara shugabanci a ƙasar.
Dr Getso ya yi wannan kira ne yayin hudubar Juma’a a Masallacin Jami’ur Rahman Jumaat da ke Kundila, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane nagari da masu cancanta ke gujewa shiga takara, lamarin da ke barin siyasa a hannun masu son zuciya da rashin kishin kasa.
“Hakkin al’umma ne su gano shugabanni nagari, su ƙarfafa musu gwiwa su nemi shugabanci, domin al’umma ta amfana da adalcinsu da gaskiyarsu,” in ji Dr Getso.
Malamin ya jaddada cewa canjin al’umma zai yiwu ne idan shugabanni masu kyakkyawan hali suka tsaya tsayin daka, tare da goyon baya da wayar da kan jama’a.
Ya kuma soki halayen wasu ‘yan siyasa da ke amfani da mulki wajen almundahana da dukiyar jama’a, inda talakawa ke ɗaukar nauyin rashin adalci da rashin shugabanci mai kyau.
Dr Getso ya bayyana muhimman siffofin shugabanci nagari, wanda ya haɗa da:
Adalci, Gaskiya, Kare dukiyar jama’a, Ƙin cin hanci da rashawa, BuɗeBuɗe ƙofa ga shawarwarin masana domin ci gaban al’umma.
Hudubar ta ƙare ne da addu’o’i na samun zaman lafiya, ci gaba, da wadata ga Najeriya baki ɗaya.
