ROLAC Ta Shirya Wa “Yan Jarida Da “Yan Fafutuka Taron Koya Dabarun Bibiyar Kasafin Kudin Jihar Kano
Daga Abdullahi Yusuf
An yi kira ga “Yan Jarida da Kungiyoyin Fafutuka na Jihar Kano da su rika bibiyar Kasafin Kudi na Jihar Kano, domin tabbatar da bin doka da gaskiya wajen aiwatar da shi.
An yi wannan kiran ne kuwa,a wajen taron koya wa “Yan Jarida da “Yan Kungiyoyin Fafutuka da ke Jihar Kano, dabarun bibiyar aiwatar da Kasafin Kudi na Jihar Kano,a ranar Litinin din nan da ta wu ce.
Wanda ya gabatar da Makala a wurin taron,Dr.Abdulsalam Kani,shi ya yi wannan kiran,in da ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da Dokokin gudanar da harkokin kudi na Jihar Kano,wato PFMLs,wajen bibiyar Kasafin Kudin.
Dr.Kani ya ce Kungiyar ROLAC ce ta bayar da taimako wajen saukaka dokokin gudanar da harkokin kudi na Jihar Kano,domin “Yan Jarida da”Yan Kungiyoyin Fafutuka su sami saukin yin amfani da su wajen bibiyar Kasafin Kudi na Jihar Kano domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen aiwatar da shi.
Daga nan sai ya shawarci “Yan Jaridar da su rika amfani da kwarewarsu ta bincike wajen bibiyar Kasafin Kudi na Jihar Kano domin tabbatar da cewa a na aiwatar da shi yadda ya kamata.
Haka su ma “Yan Kungiyoyin Fafutukar,Masanin ya yi kira a garesu da su rika bibiyar Kasafin Kudin domin tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta na aiwatar da ayyukan da ya kunsa.
Sannan kuma,Dr.Kani ya shawarci mahalarta taron da su bibiyi Kasafin Kudin domin su tabbatar da cewa a na sakin kudin da ya kunsa don aiwatar da ayyuka,sannan su hakikance an yi wadannan ayyukan.
Bugu da kari,Dr.Kani ya yi kira a garesu da su tabbatar da cewa a na gabatar da Kasafin Kudin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano a kan lokacin da doka ta tsara,sannan su tabbatar da cewa Kasafin Kudin ya kunshi ra’ayoyin da mutanen Jihar Kano su ka bayar wajen tsara shi.
Haka kuma ya shawarce su da su halarci Taron Jin Ra’ayin Jama’a wanda Majalisar Dokokin Jihar Kano za ta kirawo domin tattaunawa a kan yadda za a aiwatar da Kasafin Kudi na Jihar Kano na shekarar kudi ta 2026, wadda Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar mata.
Dr.Kani ya ce,ya kamata “Yan Jaridar da “Yan Kungiyoyin Fafutukar su bibiyi Kasafin Kudin na Jihar Kano daki-daki,domin su fada wa Gwamnati da Jama’ar Jihar Kano duk wasu matsalolin da su ka gano a cikinsa,domin a gyara domin ci gaban Jihar.
A cikin jawabinsa, Shugaban Kungiyar ta ROLAC a Jihar Kano,wadda ita ce ta shirya taron,Malam Ibrahim Bello,ya ce an kira taron ne domin a koya wa “Yan Jarida da “Yan Kungiyoyin Fafutuka dabarun bibiyar Kasafin Kudin Jihar Kano domin tabbatar da gaskiya da bin doka wajen aiwatar da shi.
Shugaban na ROLAC, wanda Isma’il Bello ya wakilta, ya ce kungiyarsa a shirye ta ke ko da yaushe, wajen yin aiki tare da “Yan Jarida da “Yan Kungiyoyin Fafutuka domin tabbatar da bin doka,gaskiya,adalci da rikon amana wajen aiwatar da Kasafin Kudi na Jihar Kano.
