Wata Babbar Kotun Kano ts soke belin da aka bai wa Kabiru Aminu a shari’ar da ta shafi duka a unguwar Danladi Nasidi, Karamar Hukumar Kumbotso.
An yanke hukuncin ne a Babbar Kotun Jiha ta 10 da ke Bompai Road, Kano, a gaban Mai Shari’a Aisha Yau, inda kotu ta amince da bukatar masu kara na soke belin bisa girman laifukan da ake tuhuma.
Ana tuhumar Kabiru Aminu da shiga harabar wani ba bisa ka’ida ba, fashi da makami da yiwa Hajiya Rabi dukka da yankarta daya haddasa raunuka.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ci gaba da bin shari’ar har zuwa karshe domin tabbatar da adalci.
Wannan na cikin wata Sanarwa da Kakakin kwamishinan shari’a na jihar Kano Abubakar Tijjani Ibrahim ya fitar.
