Kimanin Mata da kuma Yara Mata Miliyan 68 a ƙasarnan ne suka fuskanci cin zarafi ta hanyar yi musu Kachiya wanda yake nuni da cewa kimanin kaso 22 cikin Ɗari na Mata Miliyan 230 da aka yiwa Shayi a Duniya sun fito ne daga Najeriya kamar yadda aka bayyana a wani taron Bitar wayar da kai kan illlar yiwa Mata Kachiya da aka gudanar a nan birnin Kano.

A yayin da take magana a rana 3 ta taron Bitar wanda yake gudana a Otel din Tahir, wata Mai rajin kare haƙƙin Mata mai suna Hajiya Karima Bungudu ta bayyana cewa Alkaluman ƙididdigar da aka tattara kan bayanan al,amuran Lafiya da kididiga bisa yawan al,umma wato National Demographic Health Survey NDHS kan yiwa Mata Kachiya masu razanarwa ne.

Ta bayyana cewa a halin yanzu kimanin Ƙasashe 31 ne a Duniya ne abin yafi kamari wanda ya sanya Mata Miliyan Huɗu cikin Hadari. Ƙasashen da aka fi cin zarafin Matan ta hanyar yi musu Kachiyar sun haɗa da Ƙasashen Misra da Sudan da Kenya da kuma Guinea, bisa ga bayanan da aka tattara.

Hajiya Karima Bungudu ta bayyana damuwa kan yadda ake yiwa Mata Kachiya kafin cikarsu Shekaru Biyar yayin da kashi 96% suke fuskantar hakan daga baya.

Hajiya Karima Bungudu ta kuma bayyana irin illlolin da yiwa Mata Kachiya suke kawowa da suka haɗa da Jin zafi da kuma Radadi mai zafi da zubar da jini mai tsanani da kasa riƙe fitsari na dogon lokaci, da kuma sauran matsaloli masu haɗari ga kiwon lafiya na dogon lokaci.
Hajiya Karima Bungudu ta buƙaci da wayar da kan al’umma kan yadda al’adu gargajiya suke taka rawa wajen illata lafiyar “ya”ya Mata tare da horar da ma’aikatan lafiya domin saurin Gano matsalolin da yiwa Mata Kachiya suke kawowa.

