KAN DAKALI
Muna masu farin cikin gabatar muku da Dandamalinmu na sharhi a kan al’amuran Yau Da Kullum mai suna,”Kan Dakali.”Mun samo wannan suna ne daga “Dakali” wanda wani abin zama ne da a ke ginawa a kofar gidan Malam Bahaushe,inda mutane suke ke taruwa a kansa su na hira, musamman ma da dare.
A KAN DAKALI, wanda zai rika fitowa lokaci-lokaci a cikin wannan Jarida ta mu mai albarka,za mu rika yin tsokaci a kan al’amuran yau da kullum da su ka shafi zamantakewa,siyasa,tattalin arziki da sauransu,ba tare da nuna son zuciya, son kai,ko wani bangaranci ba.
Mun gode.
Naku,
Abdullahi Yusuf.