Janye “Yan Sanda Daga Gadin Masu Hannu Da Shuni Zai Inganta Aikin Dan Sanda, In Ji Tsohon Kwamishinan “Yan Sanda Balarabe Sule
Daga Abdullahi Yusuf
Wani Tsohon Kwamishinan “Yan Sanda, Alhaji Balarabe Sule,ya ce umarnin Shugaban Kasa Bola Tinubu na janye “Yan Sanda daga Gadin Masu Hannu Da Shuni za ya inganta aikin Dan Sanda ta fannoni da dama a kasar nan.
Alhaji Balarabe Sule,ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya bayyana a matsayin Babban Bako a cikin shirin Yau Da Kullum mai suna “Duniyarmu A Yau” na Gidan Radiyon Freedom da ke Kano.
Ya ce a yanzu haka,yawan “Yan Sandan kasar nan ba ya kai dubu dari hudu ba, saboda haka dawo da “Yan Sanda daga aikin kare manyan mutane zai yi alfanu wajen bunkasa aikin tsaro,in an yi la’akari da karuwar aikata manyan laifuka a kasar nan.
Daga nan kuma sai Tsohon Kwamishinan “Yan Sanda Balarabe Sule ya nuna bukatar da ke akwai ta horas da “Yan Sandan da a ka janyesu daga aikin kare manyan mutane, a kan kalubale iri-iri na tsaro wadanda kasa ke fama da su a halin yanzu.
Ya ce, wannan horon za ya inganta aikinsu na kare lafiya da dukiyoyi a cikin kasa.
Ya ce hakan kuma zai daukaka aikin “Yan Sanda a idanun “Yan Nigeria kamar yadda Tsarin Mulki ya tanada.
Alhaji Balarabe Sule, ya yi nuni da sashi na 214 na Tsarin Mulki na 1999 wanda ya fayyace aikin “Yan Sanda wanda ya hada da kare lafiya da dukiyoyin “Yan Nigeria.
Ya kara da cewa ganin yawan “Yan Sanda a lunguna da sako na kasar nan kadai, za ya sanya natsuwa da kwanciyar hankali ga “Yan Kasa.
“Tsarin Mulki ya yi bayani dalla-dalla a kan aikin “Yan Sanda.Saboda haka aikinsu za ya inganta kuma ya kara samun karbuwa ga Jama’a idan a ka dawo da su daga wajen kare lafiyar Masu Hannu Da Shuni,”in ji Tsohon Kwamishinan”Yan Sandan.
Ya ce Kwamishinan “Yan Sanda na Jihar Kano na yanzu,Dakta Ibrahim Adamu Bakori,ya yi kokari matuka wajen aiwatar da umarnin Shugaban Kasa kan janye “Yan Sanda daga Masu Hannu Da Shuni,ya na mai la’akari da yawan manyan laifukan da ke wanzuwa a Jihar Kano.
Daga nan sai ya ce ya yi imanin cewa Sabuwar Rundunar Tsaro ta Neighbourhood Watch da a ka kaddamar a Jihar Kano kwanan nan, za ta taimaka sosai wajen agazawa aikin “Yan Sanda na kare lafiya da dukiyoyi, musamman a yankunan karkara.
Alhaji Balarabe Sule,ya kuma yaba wa maye gurbin “Yan Sanda da a ka yi da Dakarun Civil Defence a wajen gadin Masu Hannu Da Shuni,ya na mai cewa wannan za ya bai wa “Yan Sanda damar mayar da hankali a kan aikinsu na kare lafiya da dukiyoyi.
Sai dai ya ba da shawarar da a rika dubawa da kula sosai da ayyukan “Yan Sandan Wucin Gadi wato “Yan Constabulary, domin a tabbatar su na bin ka’idar aikin, kuma cikin da’a.
