
Daruruwan Jama,a sun yi tururuwa a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da yammacin Asabar domin halartar jana’izar Alhaji Ado Aminu Mai Shinkafa, da aka fi sani da Alhaji Ado Lamco.

An gudanar da sallar jana’izar ne bayan sallar La’asar, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

Daga nan dandazon jama’a suka raka gawar zuwa Makabartar Ado Dandolo, inda aka yi masa sutura.

Alhaji Ado Lamco fitaccen ɗan kasuwa ne a bangaren magunguna da kiwon lafiya, kuma shi ne ya kafa kantin magunguna Lamco Pharmacy, Wanda ya shahara a fadin Kano.

Ya rasu ne a ranar Litinin, 17 ga Nuwamba 2025, a wani asibiti da ke birnin Cairo, kasar Masar, inda yake karban magani.
Ya rasu yana da shekaru 70.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana “nuna mutukar kaduwa” don gane da rasuwar, yana bayyana Ado Lamco a matsayin “dattijo Mai nagarta” wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tallafa wa al’umma.

Ya kuma ce marigayin ya kasance “fitaccen ɗan kasuwa” a fannin magunguna da harkar lafiya, wanda tarihin gudumuwarsa ba zai misaltu ba.

Alhaji Ado Lamco ya bar Yaya 15, maza 10 da mata 5 .
