Author: Abbas Ibrahim

Daruruwan Jama,a sun yi tururuwa a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da yammacin Asabar domin halartar jana’izar Alhaji Ado Aminu Mai Shinkafa, da aka fi sani da Alhaji Ado Lamco. An gudanar da sallar jana’izar ne bayan sallar La’asar, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II. Daga nan dandazon jama’a suka raka gawar zuwa Makabartar Ado Dandolo, inda aka yi masa sutura. Alhaji Ado Lamco fitaccen ɗan kasuwa ne a bangaren magunguna da kiwon lafiya, kuma shi ne ya kafa kantin magunguna Lamco Pharmacy, Wanda ya shahara a fadin Kano. Ya rasu ne a ranar…

Read More

Daga Abba Anwar Gungun wasu kwararru kan nazarin sammatsin siyasa da ci gaban ta sun gudanar da wani bincike kan wasu jagororin ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya. An yi wannan bincike ne kan dukkanin jihohin arewa 19. A binciken nasu daga cikin wadanda su ka gama tattara bayanai sun hada da jihar Kano da wasu kalilan daga jihohin arewan. A jihar Kano sai su ka zakulo mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, wato Sanata Barau Jibrin da yake wakiltar Kano Ta Arewa. Da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudunwada-Doguwa, a majalisar wakilai ta kasa, wato Alhassan Ado Doguwa.…

Read More

Danga Kwamared Abbas Ibrahim Na daɗe ina son yin wannan rubutu amma ban yi ba, ba wai saboda wani takunkumin doka ba. Domin kuwa sashi na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba da ‘yancin fadin albarkacin baki. Sai dai a halin yanzu ne na ga dacewar lokacin yin wannan rubutu. Yanzu da na yi ritaya daga aiki a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, bayan ajiye aiki a matsayin Editan Labarai a gidan Radio Kano dake zama cibiyar gwamnati da ake alfahari da ita wadda kuma za ta cika shekaru 80 da kafuwa a shekara mai zuwa — na…

Read More

Aikin Wucin Gadi: Babban Barazana Ga Ci Gaban Dan Adam Dsga Comrade Abbas Ibrahim Aikin wucin gadi ya zama babban kalubale ga ci gaban dan adam, yayin da miliyoyin ma’aikata ke tsaka da ayyuka marasa tabbaci, marasa kyau, da rashin kariya. Masana aiki na gargadin cewa wannan dabi’a, wadda ta yadu a fannoni da dama, na rage yawan aiki mai inganci, da kwanciyar hankali a cikin al’umma, da kuma ci gaban kasa a dogon lokaci. Ma’aikatan wucin gadi sau da yawa suna samun albashi kasa da na ma’aikatan dindindin, ba sa samun wasu hakkoki kamar fansho ko inshorar lafiya, sannan…

Read More