Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya sanya hannu kan Dokar Kula da Tsoffi wadda ke ba da gata na musamman ga duk ɗan asalin jihar da ya kai shekara 60 zuwa sama.
Sabuwar dokar ta tanadi
Albashi na wata-wata kyauta
Jinya kyauta a asibitoci
Sauran alawus-alawus da tallafi har zuwa rasuwa
An ce manufar dokar ita ce rage raɗaɗin rayuwa ga tsofaffi, da tabbatar da walwalarsu, da kuma basu kariya ta zamantakewa bayan ritaya ko rashin ƙarfi.
Masu sharhi na ganin matakin zai iya zama abin koyi ga sauran jihohi idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, tare da tabbatar da isasshen kasafin kuɗi da ingantaccen tsari na rarraba tallafin.
