Alhaji Aminu Baba Dan,agundi yace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bashi da wani Hurumi na bada Shawarar Janye Jami’an tsaron Gidan Sarki na Nassarawa
Yace “Maganar da take kotu to Kai waye zakayi wannan maganar a Matsayin kana wa?”
Sanarwa da Abubakar Balarabe Kofar Na, Isa ya bayar ta ruwaito Amina Babba na cewa “Baka da wani Hurumi akan wannan, kuma koshi Gwamnan Kano Bashi da wannan Hurumin.”
Sarkin Dawaki Babba ya kara da cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kotu ce ta bashi wannan tsaro ba Gwamnati ba.
A don haka ne ma yace wannan maganar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi dai dai take da zancen Teburin Mai sayar da shayi.
Sarkin Dawaki Babba yace Idan kwankwaso bai fahimta ba ya Kamata ya gane cewa irinsu da basu da mukamin komi akace a Janyewa Jami’an Sanda.
