Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (rtd), ya jaddada cewa sabon tsarin gwajin miyagun ƙwayoyi da aka kaddamar a makarantu an tsara shi ne domin rage yawaitar shan kwayoyi a tsakanin matasan Najeriya, musamman daliban da ke neman shiga manyan makarantun gaba da sakandare.
Ya bayyana cewa tsarin, wanda ya ƙunshi gwaje gwaje na dole da na bazata, mataki ne na kariya ba na hukunci ba, domin hana matasa tsunduma cikin shan miyagun kwayoyi.
Marwa ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi Zababben Shugaban Jami’ar Taraba dake (TSU), Jalingo, Farfesa Sunday Paul Bako, tare da shugabannin jami’ar a hedkwatar Hukumar NDLEA.
Ya ce shirin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da NDLEA ke jagoranta tare, wani yunkuri ne a matakin kasa baki Daya dimin tinkarar matsalar shan miyagun kwayoyi da ke karuwa a tsakanin matasa.
Janar Marwa , me ritaya , ya yi maraba da bukatar hadin gwiwa da jami’ar, inda ya yaba Mata da kuma Gwamnatin Jihar Taraba saboda samarda wani sashi na musamman don Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a jami’ar.
Yace bayyana hakan a matsayin abin koyi, tare da tabbatar da cewa NDLEA za ta ba da cikakken goyon baya ta fuskar horaswa da sauran fannoni na hadin gwiwa.
A nasa jawabin, Farfesa Bako ya yabawa jagorancin Marwa a Hukumar NDLEA, tare da taya shi murna kan sabunta wa’adin Jagorancinsa.
Ya ce ziyarar ta samo asali ne daga damuwa kan karuwan shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, lamarin da ke barazana ga nagartar ilimi, dabi’u da ci gaban kasa.
Shugaban jami’ar ya jaddada shirye-shiryen TSU na zurfafa hadin gwiwa da NDLEA a fannonin bincike, wayar da kai ga jama’a, horaswa, shirin koyon sana’oi ga dalibai da kuma ayyukan wayar da kai a al’umma.
Dukkan bangarorin biyu sun bayyana fatan cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen samar da kyakyawar yanayin karatu marar shan miyagun kwayoyi, kare makomar matasan Najeriya da kuma ba da gudummawa ga ci gaban kasa, daidai da manufar sabunta fata wato Ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
