Kungiyar Medipool Nigeria Ta Ziyarci Hukumar Samar Da Magunguna Ta Jihar Kano
Daga Abdullahi Yusuf
A cikin wani yunkuri na tabbatar da samar da Magunguna masu kyau,nagarta da saukin farashi, Kungiyar Medipool Nigeria Ta ziyarci Hukumar Samar da Magunguna da Kayayyakin Asibiti Ta Jihar Kano,wato DMCSA.
Makasudin ziyarar wadda Tawagar Kungiyar ta kai ranar Alhamis, shi ne domin inganta Tsarin samar da Magunguna cikin rahusa.
Tawagar, wadda Kafayat Babalola ta shugabanta,ta taba alli da Jami’an Hukumar ta DMCS wajen fahimtar aikace-aikacenta wadanda su ka hada da sayowa da rarraba Magunguna ta hanyoyi masu sauki da rahusa.
Madam Babalola ta ce, ziyarar ta su ta na cikin kudirin Medipool na samar da Magunguna masu rahusa cikin gaskiya da rikon amana a duk fadin Nigeria.
Ta ce samar da Magunguna masu inganci da rahusa ga Asibitocin Gwamnati ta hanya mai dorewa, abu ne mai mahimmanci,kuma kokarin DMCS a wannan aiki zai taimaka wa Medipool wajen hudda da sauran Jihohi.
Yayin da ya ke karbar “Yan Kungiyar ta Medipool, Babban Daraktan Hukumar ta DMCS,Pharm. Gali Sule,ya jaddada kudirin Hukumar na ci gaba da bunkasa ayyukanta ta hanyoyin da su ka kamata.
Pharm.Sule ya ce sauye-sauyen da Hukumar ta ke yi a halin yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da su, kuma su na kara kyautata ayyukanta.
Ya ce ziyarar ta Medipool ta mayar da hankali ne wajen yadda za a rika samar da Magunguna masu inganci da rahusa da kuma yadda za a rika rarrabasu ga “Yan Kasa.
