Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a
—Rahoto
Daga Salisu Ibrahim Fagge tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau, Abdullahi Yusuf, Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan
Kasuwancin dabbobi a Kano na kara bunƙasa cikin sauri, yayin da buƙatar nama, madara da fata ke ƙaruwa a sassan Najeriya.
Amma duk da wannan ci gaba, wani bincike na musamman ya nuna cewa ana fuskantar babbar barazana ta ɓoye wajan yawaitar amfani da wani sinadarin magani da ake kira “Sha Ka Fashe.”
Binciken ya gano cewa wasu ’yan kasuwar dabbobi na amfani da wannan sinadari domin sa shanu da tumaki su yi kiba cikin gaggawa, don su jawo hankalin masu saye a kasuwa.
Rahotanni sun nuna cewa “Sha Ka Fashe” da aka fi dangantawa da ƙara kiba a jikin ɗan adam, yanzu ana ba dabbobi domin su yi girma cikin kankanin lokaci.
Masana sun yi gargadin cewa hakan na iya cutar da lafiyar jama’a, domin samuwar magunguna a nama na iya haifar da matsaloli masu tsanani, ciki har cututtuka.
Wasu masu sayen dabbobi sun koka da asarar dukiya bayan sayen dabbobin da suka bayyana masu ƙoshin lafiya, amma daga baya su kamu da rashin lafiya ko su mutu cikin gaggawa.
Malam Muhammad Balarabe ya ce ya sayi saniya mai ƙiba da ƙarfi a gani, amma cikin kwanaki kaɗan ta kamu da gudawa mai tsanani kuma ta mutu. Ya ce irin wannan lamari na buƙatar matakin gaggawa daga gwamnati.
Jami’an Hukumar Kula da abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC sun ce sun kama magungunan jabu, sun rufe masana’antun da ke samar da magungunan dabbobi ba tare da rajista ba, tare da gurfanar da masu laifi a kotu.
Haka kuma ma’aikatar kula da kiwon dabbobi ta jihar na ƙara yin rajistar wuraren kiwo da bibiyar masu sayar da magungunan dabbobi domin inganta tsaron lafiyar jama’a.
Masana da masu ruwa da tsaki sun ce idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, matsalar za ta iya zama barazana ga lafiyar jama’a, tattalin arziki da Kuma samar da abinci.
Sun buƙaci a tsauraran dokoki kan amfani da magungunan dabbobi,
wayar da kan jama’a kan haɗarin nama maras inganci, tallafa wa manoma masu bin ƙa’ida,da kafa mayanka na halal da ƙwararru za su kula da su.
Yayin da kasuwancin dabbobi ke ci gaba da bunƙasa a Kano, jama’a na fatan a ɗauki mataki cikin gaggawa domin hana wannan matsala ta zama barazana ga rayuwar al’umma.
