´
Taron jama’a mai yawa ne , safiyar ranar Talata yayi Tururuwa domin halartar jana’izar Muhammad Sani Hassan, wanda aka fi sani da Sanin Kale, a unguwar Yakasai da ke cik
in ƙaramar hukumar Municipal.
Sanin Kale, wanda bai yi wata rashin lafiya ba, ya rasu ne bayan ya kammala sallar Isha’i.
Ƙanwarsa, Zainab Hassan wadda aka fi sani da Ta’annabi, ta bayyana cewa Sani, wanda ya shahara a unguwar, ya yi wasa da yara tare da raba musu alewa kaɗan kafin rasuwarsa.

Wani mazaunin yankin, Mohammed Yakasai, ya ce:
“A nan kusa bamu ga irin wannan taron jama’a mai yawa a jana’iza a wannan yanki ba, Sanin Kale nada kyakyawar mu,amala, Allah ya gafarta masa ”



Marigayi Sanin Kale, mai shekaru 60, ya bar mace daya, ’ya’ya bakwai, tare da sauran ’yan uwa da suka haɗa da Auwal Hassan wanda aka fi sani da Omosee, da kuma Zainab Hassan (Ta’annabi).
A halin yanzu, jama’a na ci gaba da tururuwa zuwa gidansa domin yin ta’aziyya.
