Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO
Daga Abdullahi Yusuf
Wata ƙungiya mai zaman kanta ta bayyana damuwa kan yadda yawaitar kananan yara masu rayuwar titi ke ƙaruwa a Kano, inda ta ce adadinsu ya haura miliyan biyu.
Ƙungiyar Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa dubban yara na kwana a tituna da wuraren jama’a a kowace rana, cikin yanayi mara tsafta da rashin tsaro.
Babban Daraktan ƙungiyar, Mohammed Ali Mashi, ya shaida wa manema labarai cewa da dama daga cikin yaran ana aiko su ne daga ƙauyuka ko jihohin maƙwabta domin neman ilimin addini, amma sakamakon yunwa da rashin kulawa suna barin karatu su rungumi rayuwar titi.
Ya ce irin wannan rayuwa na jefa yara cikin haɗarin cin zarafi, aikata laifi da kuma rikici da doka, yana mai gargadin cewa matsalar na iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati, shugabannin al’umma da malamai su haɗa kai domin samar da mafita, ciki har da matsuguni, ilimi, abinci da kulawar lafiya ga yaran.
Haka kuma ta jaddada buƙatar rage talauci a karkara da wayar da kan iyaye kan muhimmancin kulawa da ‘ya’yansu, tana mai cewa dole ne neman ilimi ya tafi tare da kare lafiyar da jin daɗin yara.
GIOPPINI ta yi gargadin cewa rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa na iya haifar da ƙarin matsalolin zamantakewa da na tsaro a nan gaba.
