An Kaddamar Da Kungiyar Ci Gaban Tarauni,Daurawa Da Farm Centre
Daga Abdullahi Yusuf
A ranar Al’hamis din nan ne a ka kaddamar da Kungiyar Ci Gaban Tarauni,Daurawa Da Farm Centre, don bunkasa tattalin arziki da jin dadin mutanen yankin.
An yi bikin kaddamarwar ne a Ofishin Shiyyar Arewa Maso Yamma na Cibiyar Koyar da Fasahar Kyankyasa Ta Kasa da ke Farm Centre a Kano.
Kungiyar Rayawa da Ci Gaban Al’umma ta Kano,wato KCDS ce ta shirya taron na kwana daya.
A cikin jawabinsa, Shugaban Kungiyar ta KCDS, Farfesa Muhammad Tabi’u,ya ce makasudin kaddamar da Kungiyar ta Ci Gaban Tarauni, Daurawa Da Farm Centre shi ne domin a samar da tsaro,ci gaban tattalin arziki da walwalar mutanen yankin.
Tabi’u ya ce, hakan ya zamo dole saboda bullar matsalolin tsaro da su ka hada da sace-sace,kwacen waya,shan kwaya da fyade tsakanin matasa da sauransu, a wadannan unguwannin da makwabtansu.
Ya ce abin takaici ne ganin cewa Kano da ta shahara wajen kasuwanci, ilimi da al’adu sai ga shi ta na fama da matsalolin tsaro da makamantansu.
Domin magance wadannan matsaloli, in ji Shugaban,sai a ka kirkiro wannan Gidauniya domin mutane su taimaka da kudi daidai karfinsu.
Ya ce kowa na iya bayar da abin da ya saukaka,kuma a kowanne lokaci, don cinma burin da a ka sanya a gaba.
Farfesa Tabi’u ya ce hakan ya zamo dole saboda Gwamnati kadai ba za ta iya biya wa mutane dukkan bukatunsu ba.
Ya ba da tabbacin cewa duk kudaden da a ka tara a cikin Gidauniyar za a yi amfani da su cikin gaskiya, rikon amana da tsoron Allah.
Shi ma a cikin jawabinsa,Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi II, ya koka game da yadda a ke samun karuwar shan miyagun kwayoyi a Kano, musamman tsakankanin matan aure da matasa.
Sarkin, wanda Hakimin Tarauni, Alhaji Bello Bayero, ya wakilta,ya ce wannan abin takaicin ne ya ke jawo yawan aikata laifuka kamarsu fyade,sace-sace,kwacen waya da kisan kai a yankin.
Saboda haka, Sarkin ya yi maraba da kaddamar da wannan Kungiya, wadda ya ce za ta taimaka matuka wajen magance wadannan matsaloli.
