Jam’iyyar African Democratic Party (ADC) ta soki dokar gyaran haraji ta Gwamnatin Tarayya, inda ta bayyana ta a matsayin wadda ke cutar da al’umma tare da barazanar jefa kasar cikin karin matsin tattalin arziki da rashin daidaiton zamantakewa.
Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a sassan kasar, inda ta bayyana cewa halin da ake ciki a matsayin abin tausayi da ke kara haifar da rashin aminci tsakanin jama’a da gwamnati, sakamakon kasa cika alkawuran da aka sha yi na kare rayuka da dukiyoyi.
Wadannan batutuwa na kunshe ne a cikin sakon Kirsimeti da jam’iyyar ta aikawa ‘yan Najeriya, wanda Mataimakin Sakataren Tsare Tsare na kasa na jam’iyyar, Ali Tukur Gantsa, ya sanya wa hannu. A sakon, ya mika sakon taya murna ga Kiristoci tare da addu’ar samun zaman lafiya da wadata a Sabuwar Shekara ga dukkan ‘yan Najeriya.
Gantsa, tsohon Sakataren Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Jigawa kuma Sakataren Tsare Tsare na Yankin Arewa maso Yamma na ADC, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata ta hanyar daukar matakan gaggawa kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.
Ya kuma jajanta wa Gwamnati da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar guda biyu a rana guda, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin alhini da babban rashi ga jihar da ƙasa baki ɗaya.
Haka zalika, ADC ta jajanta wa Gwamnatin Jihar Borno da iyalan wadanda abin ya shafa sakamakon harin kunar bakin wake na baya-bayan nan da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama tare da jikkata wasu da yawa ADC tayi kira da gwamnatin Tarayya ta kara jajircewa wajen kare lafiyar ‘yan ƙasa.
A ƙarshe, jam’iyyar ta yi kira da a rungumi hadin kai, tausayi, da shugabanci na gari biyan bukatun jama’a yayin da ‘yan Najeriya ke bikin Kirsimeti tare da fatan shiga Sabuwar Shekara cikin kwanciyar hankali.
