Shugabar Hukumar Kula da Tsarin Kiwon Lafiya na taimakekekiya ta Jihar Kano (KSCHMA), Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta yi kira da a karfafa hadin gwiwa da shugabannin mata a kungiyoyin kwadago domin fadada wayar da kai da kuma amfanin shirin inshorar lafiya na jihar.
Dakta Rahila Mukhtar ta bayyana hakan ne yayin da ta halarci Taron Tsare-tsaren Dabaru na Shugabannin Kwamitin Mata na Ƙungiyoyin Kwadago yayinda taron ke gudana . Duk da cewa ta isa taron ne a tsakiyar shirin, ta gabatar da cikakken bayani kan Tsarin Inshorar Kiwon Lafiya na Jihar Kano, inda ta yi bayani kan ayyukansa, manufofinsa, da sauran tsare tsare.
Taron ya haifar da tattaunawa mai Jan hankali, inda mahalarta suka nuna farin ciki tare da damuwa, musamman lokacin da Dakta Rahila ta yi bayani kan nauyin da ke kan asibitocin dake cikin shirun da kuma hakkoki da damammakin waddanda ke anfana da shirin . Daga bisani, ta yi alkawarin shirya wani taron wayar da kai na musamman ga sama da mata shugabanni 100 da suka halarci taron, domin kara fahimtar shirin sosai .
A cewarta, taron da Zata dauki nauyi , zai ba shugabannin mata na kwadago karin ilimi da sahihan bayanai da za su taimaka musu su zama jakadu na wayar da kai kan fa’idar shirin.
Tun da farko, Shugabar Kwamitin Mata, Comrade Rabi Muhammad, ta bayyana taron a matsayin irinsa na farko , tana mai cewa zai zama wata muhimmiyar hanya ta haɗin gwiwa da sadarwa ga mata masu fafutukar kare muradun ma’aikata, tare da ƙarfafa muryarsu kan walwalar jama’a da kariyar zamantakewa.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Musa, wanda wani Babban Sakatare , Alhaji Salisu Mustapha ya wakilta, ya jaddada muhimmiyar rawar da kungiyoyin kwadago ke takawa wajen karfafa nagartar aiki.
Haka kuma, Shugaban Kungiyar Kwadago (NLC) reshen Jihar Kano, Comrade Kabiru Inuwa, ya sake jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da kyakyawar yanayin gudanarda aiki a jihar kano.
Shugaban makarantar kwadago na kasa Dakta Muntaka Yushau ya gabatarda makala Mai tsawo akan gwagwarmaya a kwadago.
Ita ma tsohuwar ma,ajin Kungiyar kwadago ta Kano Kwamared Munubiya a makalar data gabatar ta yi bayan akan hadin kai a gwagwarmaya.
A karshen taron, Mataimakin Shugaban Kungiyar kwadago na kasa, NLC kuma Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya (MHWUN), a matakin kasa,Comrade Kabiru Ado Minjibir, ya rabawa mahalarta taron takardar shaidan halarta.
