Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da tsarin gwajin shan ƙwayoyi na dole a matsayin sharadi ga duk wanda ke neman aiki a tarayya.
Masu ruwa datsaki da dama sun bayyana matakin, abun da ya dace domin yaki da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
Wannan tsari, wanda ya shafi masu neman aiki, na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na karfafa gaskiya, tsaro da kwarewa a cikin hukumomin gwamnati tare da rage barazanar da shan miyagun kwayoyi ke haifarwa.
Da take martani kan wannan batu, shugabar Kungiyar dake yaki da Shan Miyagun kwayoyi wato , League Of Societal Protection Against Drug Abuse (LESPADA), Ambasada Maryam Hassan, ta yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa daukar wannan muhimmin mataki na kare ma’aikata da makomar Najeriya.
A cewarta, shan miyagun kwayoyi na ci gaba da zama babbar barazana ga iyalai, hukumomi da kuma cigaban kasa baki daya.
“Mayar da gwajin shan kwayoyi sharadi kafin samun aiki zai taimaka wajen karfafa dabi’a nagari, tabbatar da tsaron wuraren aiki, da samar da ma’aikata marasa shan miyagun ƙwayoyi,” in ji Ambasada Maryam Hassan. “Wannan tsari ba wai na aiki kadai ba ne, illa dai na kare al’umma baki ɗaya.”
Ta kuma jaddada cewa ya dace a fadada wannan tsari fiye da batun aiki, ta hanyar shigar da shi cikin shigar dalibai makarantun sakandare da na gaba da sakandare, da kuma kafin aure, kamar yadda ake yi wajen gwajin Kwayoyin halitta, wato (genotype) da na lalurar dake karys karkuwan jiki wato HIV.
“Gano matsala da wuri da kuma daukar matakin gaggawa na iya ceton rayuka, kare iyalai, da hana mummunan tasiri na dogon lokaci,” in ji ta.
Ambasada Maryam Hassan ta bayyana wannan tsari a matsayin wata alama mai karfi ta kudurin gwamnati na yaki da shan miyagun kwayoyi, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da cibiyoyin ilimi, kungiyoyin addini, da kungiyoyin farar hula da su mara wa shirin baya tare da tabbatar da dorewarsa.
Ta kammala da yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa yin tsayuwar daka, tana mai cewa hadin kai tsakanin kowa da kowa ne zai haifar da kasa mai lafiya, tsaro, da cigaba mai dorewa.
