Daga Abba Anwar
Gungun wasu kwararru kan nazarin sammatsin siyasa da ci gaban ta sun gudanar da wani bincike kan wasu jagororin ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya. An yi wannan bincike ne kan dukkanin jihohin arewa 19.
A binciken nasu daga cikin wadanda su ka gama tattara bayanai sun hada da jihar Kano da wasu kalilan daga jihohin arewan. A jihar Kano sai su ka zakulo mataimakin shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, wato Sanata Barau Jibrin da yake wakiltar Kano Ta Arewa. Da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudunwada-Doguwa, a majalisar wakilai ta kasa, wato Alhassan Ado Doguwa.
Manazartan sun yi ittifakin cewa su wadannan jiga-jigan jagororin daga Kano, sune yan siyasar da su ka fi shan tsangwama. Amma cikin Ikon Allah kullum likkafarsu gaba take kara yi. Ko jama’a sun fahimci hakan ko ma ba su fahimci hakan ba. Sun ce su dai sakamakon bincike ne ya nuna musu hakan.
Kuma babban abinda su ka gano shine, wannan tsangwama din, su na fama da ita ne, daga cikin jam’iyyarsu da kuma wajen jam’iyyar tasu, daga ‘yan adawa na waje kenan. Akwai nuni da yadda a ke tsangwamarsu da yi musu kulle-kulle da kuma shirya musu mugun tanadi. Amman duk da hakan sai kara samun daukaka suke daga Allah.
Haka nan wannan binciken ya nuna cewar shi Sanata Barau ya fara samun tsangwama ne fa tun kasancewarsa dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Tarauni a shekarar 1999. Karkashin jam’iyyar PDP. Lokacin marigayi Ghali Umar Na’Abba ya na Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa.
A lokacin Barau din ya na shugabancin Appropriation Committee a majalisar wakilan.
A wancan lokacin ya na daga cikin yan majalisar da su ka fi kusanci da Kakakin Majalisar. Kuma tsangwamar fa a lokacin ya same ta ne daga cikin jam’iyyarsa ta PDP.
Har ta kai ta kawo a zaben 2003 a kai masa kutingwuila ya fadi zabe. Shi da marigayi Na’Abban. Wanda su ma su ka yi sanadiyar faduwar Gwamna mai ci a lokacin, wato Rabi’u Musa Kwankwaso a dai wannan zaben. Daga nan Malam Ibrahim Shekarau na ANPP ya samu nasarar zama gwamna.
Masu wannan bincike sun gano cewar a tarihin siyasar Kano ba wani dan siyasa da ya taba tsallakawa daga dan majalisar tarayya zuwa majalisar dattawa, a shiyyoyi daban daban kuma ya samu nasara da fice da zarra kamar Sanata Barau ba.
Bayan ya sha makirci da kulle-kulle a 2003, sai ya tsallaka daga Tarauni, wacce take Kano Ta Tsakiya, ya tafi Kano Ta Arewa, ya tsaya takarar Sanata, kuma cikin Ikon Allah ya samu nasara. Shi kadai ne haka ta fara faruwa da shi a cikin jagororin yan siyasa kuma yan majalisa daga jihar Kano.
Wani abin ban sha’awa da ban mamaki kuma shine, ko a tsayawar tasa ta Sanata daga Kano ta Arewa, a nan ma ya sha wahala kuma ya ga abubuwan da ya gani na nuna adawa da kiyayya da tsana da tursasawa daga cikin gida.
Amman fa da hakan cikin Ikon Allah sai ga shi ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa. A tarihin siyasar Kano, shine wanda ya fara rike mukamin daga Kano. Kuma fa kafin ma ya samu tikitin tsayawa takarar Sanata a karo na biyu, wanda daga nan ne ya samu Mataimakin shugaban majalisar dattawa, sai da sha bakar wahala. Har ta kai sai da ya tabo alli da can sama kololuwa a tsarin siyasar Najeriya.
Daga cikin abubuwan da wannan bincike ya gano shine, yadda tun farkon farawa daga kasancewar Sanata Barau dan majalisar tarayya a 1999 kawo yanzu da yake matsayin Sanata, mutum ne da ya damu da cigaban al’ummar sa da kuma jihar sa.
An yarda cewar ko daga wancan lokacin, ya tallafawa rayuwar al’umma ta hanyoyin ba su jari dan dogaro da kai, da kuma daukar nauyin karatun su a manyan makarantu. Baya ga giggina ajujuwan karatu da makarantu da kuma tallafawa makarantun firamare da sakandare da kayan aiki. Gami da tallafawa malamai a wadannan makarantu.
Binciken ya kara yabawa Sanatan tun daga lokacin da ya zama Sanata, yake daukar nauyin karatun dalibai dan karo karatu a manyan jami’o’in kasar nan, irin su Bayero University, Kano da University of Lagos da Ahmadu Bello University, Zaria da University of Ibadan da Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, da University of Maiduguri da dai sauran manyan jami’o’i a kasar nan.
Bai ma kuma tsaya a nan ba, ya dauki nauyin dalibai guda 70 da ya tura su kasashen waje dan yin karatun Digiri na Biyu a fannonin zamani da duniya ke alfahari da fannonin.
Haka nan bincike ya kara yabawa da Sanata Barau wajen ganin yadda yake kai wa gwauro ya kai mari wajen kara inganta harkar tsaro a jihar Kano. Sun bayyana irin tallafin motocin aiki da yake ta rabawa hukumar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano. Tare da rarraba baburan hawa ga jami’an yan sanda dan kara inganta harkar tsaro a jihar. Baya ga wasu abubuwan tallafawa harkar tsaro da bai kamata a fade su a bainar jama’a ba. Saboda yadda tsaro ke son sirri.
Sun kuma dan tabo maganar kawo Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma da gwamnatin tarayya ta yi. Tare da yin tsokaci kan irin kokarin da Sanatan ya yi a wannan bangare. Baya ga kawo jami’ar kimiyya da fasaha ta Kabo. Da kuma sauran manyan abubuwan ci gaba da ya kawowa jihar sa da yankin sa na Arewa ma gaba daya. Barau ka cika gwarzo!
A nasa bangaren kuma Doguwa an tabbatar cewar a lokacin da a ka yi zaben 2023 wanda ya samu cin nasarar zabensa, ya na cikin jajirtattun yan siyasa a jihar Kano, wadanda da taimakon Allah suke kwatarwa da kansu hakki da kan su.
Da farkon farawa tukuna, shi kadai ne dan majalisar wakilai da ya ci zaben sa a 2023 daga shiyyar Arewa maso Kudu a karkashin jam’iyyar APC. Yayin da jam’iyyar NNPP ta cinye dukkan ragowar yan majalisar daga wannan yankin. Shi daya tilo. Wanda kuma zaben nasa ya sha cece-kuce bayan fadar sakamakon zaben.
Irin balahirar tsangwamar da ya sha daga ciki da wajen jam’iyyarsa kadai ya isa ya tsorata dan siyasa mara tsari kuma raggo mara gogewa. Amman cikin Ikon Allah haka ya sha bakar wuya, kusan a ce shi kadai din sa, ba tare da wani budadden tallafi daga uwar jam’iyya ba ko jiga-jigan jam’iyya. Sai dai wadanda ba a rasa ba, ‘yan kalilan.
Doguwa ya kasance, kamar yadda binciken nan ya nuna wani gwarzo kuma jajirtacce kuma babban jagora abin dogara. In dai a na maganar sanin ‘yancin kai ne da kuma gwarzanta. Wadannan wasu halaye ne ba wanda ya isa ya cire shi daga kai. Ko daga jam’iyyun adawa. Ko kuma daga ‘yan adawarsa na cikin jam’iyyar sa ta APC.
Wannan binciken ya kara nuni da cewa daga Barau har Doguwa kowannensu karansa ne yake kara kai tsaiko. Kowannensu cikin taimakon Allah, sai kara habaka yake. Saboda haka, binciken ya nuna cewar su wadannan jagorori guda biyu ba wani abu na bangaren tsangwama da kiyayya da shirya gadar zare da zai zame musu wani abu sabo a siyasa.
An ce su kadai ne za su iya gaya maka irin bakin matsin da su ka sha a hannun ‘yan siyasa. Musamman a hannun mutanen su. Kamar dai yadda masu iya magana ke cewa, ko ma dai menene zai je ya zo, to lokaci ne alkali.
Anwar ya rubuto wannan ne daga Kano,
Litinin, 17 ga watan Nuwamba, 2025
