Danga Kwamared Abbas Ibrahim
Na daɗe ina son yin wannan rubutu amma ban yi ba, ba wai saboda wani takunkumin doka ba. Domin kuwa sashi na 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba da ‘yancin fadin albarkacin baki. Sai dai a halin yanzu ne na ga dacewar lokacin yin wannan rubutu. Yanzu da na yi ritaya daga aiki a ranar 1 ga Nuwamba, 2025, bayan ajiye aiki a matsayin Editan Labarai a gidan Radio Kano dake zama cibiyar gwamnati da ake alfahari da ita wadda kuma za ta cika shekaru 80 da kafuwa a shekara mai zuwa — na ga dacewar yin nazari kan ka’idojin da ya kamata su jagoranci aikin gwamnati.
Manyan ma’aikatan gwamnati suna rike da amana da nauyi. Ayyukansu suna da tasiri na kai tsaye ga rayuwar jama’a, kamar yadda kuma suke shafar muhibbar gwamnati. Idan sun yi aiki yadda ya dace, sun cancanci yabo. Idan kuma sun ci amana, dole ne alhakin hakan ya rataya a wuyansu. Zargi bisa kasawa da kuma yabo bisa abin kirki dukkansu hanyoyi ne na karfafa da’a da gaskiya da kuma bin doka—wadanda su ne ginshikan mulkin dimokuraɗiyya.
A wata maƙalarsa, Ambasada Abdullahi Adamu Bakoji, tsohon jami’in tsaro kuma Daraktan Asusun Kula da Kare Hakkin Dan adam (IHRC-RTF) na ƙasar nan ya fayyace batun, inda ya ce:
“Aikin Gwamnati wata muhimmiyar amana ce. Wajibi ne a yaba wa duk wadanda su ka yi aikin ƙwarai. Haka kuma duk wadanda suka gaza sauke wannan amanar dole ne su fuskanci hukunci. Wannan ita hanya daya tilo ta ƙarfafa yin abin da ya dace tare da dawo da ƙwarin gwiwar da jama’a ke da shi ga shugabanci.”
Hakika, yabawa bisa riƙon amana da suka bisa cin amana tagwayen abubuwa ne da ke dawo da amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati. Tsohon karin maganar dake cewa, “Soja na zuwa kuma soja na tafiya amma bariki a koda yaushe yana nan,” yana tunatar da kowanne ma’aikacin gwamnati cewa tarihi ba ya shudewa, haka zalika ma sunan da mutum ya bari.
Daya daga cikin manyan ma’aikatan da ke zama abin koyi ta fuskar da’a da zuwa aiki a kan lokaci da kuma adalci shi ne Alhaji Abdullahi Musa, Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Jihar Kano. Kyakkyawan sunansa a fannin gudanar da aiki yadda ya dace ya samo asali tun sadda yake a Hukumar Bin Diddigin Aiki wato Due Process Bureau, inda ya sauya fasalin hukumar zuwa abin koyi ta fannin gaskiya da kirkire-kirkire.
Ina iya tuna tattaunawa game da shi da wani aboki aiki, a lokacin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sunusi Abdullahi Kofar Na’Isa. Mutane da dama suna kiran Alhaji Musa da “Karfen da ba ya tankwaruwa.” Kuma tabbas wannan suna ya dace da halayensa—tsayin daka kan aiki da nuna ƙwarewa da jajircewa wajen bin ka’ida.
Akwai abubuwan da na gani da idona da suka tabbatar min da haka. A wata rana ya aiko min da sakon zuwa don ganawa da shi da ƙarfe 8 na safe. Na iso ƙarfe 7:30, amma sai na samu tuni yana teburinsa yana cikin aiki. Da aka shigar da ni da ƙarfe 8, mun gaisa cikin fara’a sannan yace, “Toh, Malam Abbas, me kake bukata? Lokaci tsada gare shi.” A cikin mintuna goma kacal mun kammala komai. Na fita ina tunanin yadda aikin gwamnati zai inganta idan kowane jami’i yana bin irin wannan tsari.
A wani lokaci, wani babban dan siyasa ya nemi wata alfarma wadda ta saba wa ka’idar aikin gwamnati. A cikin girmamawa Alhaji Musa ya ƙi amincewa, yana mai cewa dole a bi ka’ida. Wannan abu ya bani mamaki da gamsuwa matuƙa.
Wasu na cewa yana da “tsauri sosai” ko kuma su ce “tsarinsa ya yi yawa,” amma waɗannan halaye ne da ke tsare mutuncin hukumomin gwamnati.
Akwai wata rana, ina gaggawar shiga jarabawar karin girma, na manta hula ta a mota. Da ya gan ni a lokacin yana aikin sanya ido kan Jarabawar sai ya ce, “Abbas, ba zan bari ka rubuta jarabawa a haka ba. Idan ka sanya manyan kaya, dole shigar ka ta zama cikakkiya.” Nan take na koma da sauri na ɗauko hular, na dawo cikin lokaci. Sakon shi ne: kwarewar aiki na farawa ne da koyawa kai da’a.
Haka ma wani lokaci an samu zarge-zargen saba ka’idar aiki a kan wani babban jami’in gwamnati. Galibi sun yi fargabar wani mummunan abu. Amma bayan nazari kan lamarin, Alhaji Musa sai ya ce masa: “Ka je ka warware abin da ya jawo wannan matsalar. A matsayin mu na ma’aikata, dole ne mu kare mutuncinmu da kuma na hukumar da muke yi wa aiki.” Nasiha mai cike da hikima da nutsuwa wadda ta kawar da damuwa, abin da ke nuna salon jagoranci na gari.
Bayan kusan shekaru talatin ina aikin jarida tare da mu’amala da manyan ma’aikatan gwamnati, zan iya cewa irin su Alhaji Abdullahi Musa sun cancanci a yaba musu. Domin kuwa ka’idar ita kuwa ita: Idan ka gaza taimako, kar ka cutar.”
Kowanne dan’adam tara yake, bai cika goma ba. Babu wani cikakke sai Allah Madaukaki Shi kadai. Amma duk wanda ke kokarin yin aiki cikin gaskiya da da’a da rikon amana ya cancanci yabo da girmamawa.
Kwamared Abbas Ibrahim
Mai fafutukar kare haƙƙin mata da yara, daga jihar Kano.
