Kuncin Rayuwa Ya Hana Samari Aure
Daga Abdullahi Yusuf
An ce, “Aure Yakin Mata.” Yanzu an wuce wannan wurin.Yanzu Aure ya zama “Yakin Maza,” domin kuwa a halin yanzu, Aure ya gagari Mazaje da dama, musamman ma “Samari “Yan Lalle.”
Abin damuwa da takaici ne halin da Samari su ka shiga a kasar Hausa na rashin sukunin yin Aure.Yanzu Samari a wannan shiyya ta mu ta Arewa, musamman a garuruwanmu na Hausawa, ga su nan a yashe,sun balaga,sun kai,sun kawo,su na matukar bukatar Aure,amma babu hali.
Yawancinsu sun yi karatun Boko sun gama,wadansu a cikinsu ma sun hadu da “Yanmata tun a Makaranta,sun yi soyayya har sun rabu.Yanzu sun dawo cikin unguwanninsu sun hadu da wadansu “Yanmatan sun sake bude wani sabon Babin na soyayya,amma duk ba halin yin Aure.
Binciken da wannan Sabuwar Jarida, Anzowajen, ta yi, ya gano dalilai masu kwari da su ka hana wadannan Bayin Allah sukunin yin Aure.
Daga cikinsu akwai Rashin Aikin Yi.Binciken ya gano cewa, yawancin wadannan Samari ba su da aikin yi, kuma da yawansu sun ki su yi Sana’a,wai su na jiran Aikin Ofis.Haka ne ya sa su ka rasa kudin da za su nemi Aure da su.
Wadansun su kuma sun tsorata ne da tsadar da Aure ya ke da ita a halin yanzu, musamman akwatunan Aure,kama wajen taron biki da kama Amarya.Shi ya sa irin wadannan Samari su ke yin baya-baya da Aure.
Rashin Mahalli da tsadar kudin haya su ma su na hana Samari yin Aure,domin hidimomin biki daban,sannan kuma fafutukar neman wajen da za a ajiye Amaryar daban.
Wadannan matsalolin su su ka sanya yawancin Samarinmu a kasar Hausa su ka ma hakura da Auren,su ka mayar da al’amarinsu ga Allah(SWT) ta hanyar yin Azumi da sauransu.
Wannan hali da Samarin su ka shiga,ba karamar matsala ba ce,domin kuwa Abu ne mai hadari ga Al’umma a ce ga tarin Samari kuma balagaggu a cikinta,ba su da Aure, kuma ba su da ranar yinsa.
“Yar sa’ar da a ka yi kawai ita ce, yawancin Samarin su na sha’awar kallon Kwallon Kafa, wadansu ma a cikinsu su na buga Kwallon.Wannan harkar ta kan dauke musu hankali daga son mata.Allah Ya kawo mana dauki,amin.
