Author: Abdullahi Yusuf

Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu Daga Abdullahi Yusuf Allah Mai yi da a yi,wai yanzu a kasata ta gado, Nigeria,an wayi gari man fetur ya wadata,har ma ya yi yawa,kamar ya biyo masu ababan hawa har gidajensu. Wai a yau,man fetur din da a da a ke nema kamar Ruwan Bagaja, sai ga shi yanzu a na neman kai da shi,masu gidajen mai su na kira,wani zubinma har da rokon masu ababan hawa,domin su zo su saya. Idan kuma an saya din,sai ka ga masu sayarda fetur din su na ta fara’a da godiya,kamar ba…

Read More

Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu Daga Abdullahi Yusuf Allah Mai yi da a yi,wai yanzu a kasata ta gado, Nigeria,an wayi gari man fetur ya wadata,har ma ya yi yawa,kamar ya biyo masu ababan hawa har gidajensu. Wai a yau,man fetur din da a da a ke nema kamar Ruwan Bagaja, sai ga shi yanzu a na neman kai da shi,masu gidajen mai su na kira,wani zubinma har da rokon masu ababan hawa,domin su zo su saya. Idan kuma an saya din,sai ka ga masu sayarda fetur din su na ta fara’a da godiya,kamar ba…

Read More

An Kammala Taron Sanin Makamar Aiki Na Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano A Kaduna Daga Abdullahi Yusuf A yau,16 ga watan Nuwamba 2025, ne a ka kawo karshen taron Sanin Makamar Aiki na Kungiyar Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano,wato Correspondents’ Chapel,a garin Kaduna. A lokacin taron na kwana biyu, masana sun gabatar da Makaloli dabam-dabam wadanda suka nusar da Wakilan hanyoyin da za su inganta aikinsu na rubutawa da buga labarai. Daga cikin Makalolin har da wadda Dr.Aminu Ibrahim Shehu,wanda ke aiki a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke Kano,wato AKTH, ya kawo, wadda…

Read More

Tsokaci Kan Alamun Tsufa Daga Abbas Ibrahim Kwararru masu kula da masu cutar sankara,wato cancer, a harshen turanci,sun yi tsokaci a kan irin alamun da Dan Adam ya ke nunawa idan Tsufa ya zo masa. Alamun,in ji masanan,sun hada da canje-canjen halaye da kuma kalubalen zamantakewa wadanda da ke tattare da yanayin Tsufa. Suka ce,shi Tsufa ya na fara zuwa ne daga lokacin da mutum ya cika shekaru 60 da haihuwa,daga nan zai yi ta tsufa har ya kai zuwa shekaru 80,90 har inda Allah Ya so. Daga nan sai masanan su ka ce Kadaici ya na daga cikin matsalolin…

Read More

Kwararren Likita Ya Shawarci “Yan Jarida Kan Lafiyar Kwakwalwa Daga Abdullahi Yusuf Wani kwararren Likitan kula da Lafiyar Kwakwalwa,Dr. Aminu Ibrahim Shehu, ya shawarci “Yan Jarida da su rika lura da lafiyar kwakwalwarsu sosai, domin cigaban aikinsu. Dr.Aminu Ibrahim Shehu,wanda ke aiki a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke Kano,wato AKTH,ya ce hakan ya zamo dole,in an yi la’akari da yawan samun korafe-korafen galabaita da damuwar kwakwalwa a tsakanin “Yan Jarida. Ya ba da wannan shawarar ne a yayin da ya ke gabatar da wata Makala a kan galabaita da damuwar da “Yan Jarida ke fuskanta yayin gudanar…

Read More

Kuncin Rayuwa Ya Hana Samari Aure Daga Abdullahi Yusuf An ce, “Aure Yakin Mata.” Yanzu an wuce wannan wurin.Yanzu Aure ya zama “Yakin Maza,” domin kuwa a halin yanzu, Aure ya gagari Mazaje da dama, musamman ma “Samari “Yan Lalle.” Abin damuwa da takaici ne halin da Samari su ka shiga a kasar Hausa na rashin sukunin yin Aure.Yanzu Samari a wannan shiyya ta mu ta Arewa, musamman a garuruwanmu na Hausawa, ga su nan a yashe,sun balaga,sun kai,sun kawo,su na matukar bukatar Aure,amma babu hali. Yawancinsu sun yi karatun Boko sun gama,wadansu a cikinsu ma sun hadu da “Yanmata…

Read More

Muna Gabatar Da Sabuwar Jaridarmu Ta Hausa Mai Suna: An zo wajen A duk rayuwar Dan Adam,a kan sami al’amura ko na Zamantakewa,ko na Tattalin Arziki,ko na Siyasa,wadanda su ka sha kan mutane,wadanda kuma a ke ta Muhawara a kansu domin a sami masalaha ko matsaya. Da zarar an sami daidaito a kan wani Mauru’i sai ka ji a na cewa,”An zo wajen.” Haka kuma duk lokacin da Jama’a su ke jiran wata sanarwa a kan wani abu muhimmi,ko wani Albishir,to, da zarar an sanar da shi,sai ka ji an ce, “An zo wajen.” Jama’ar Arewa sun dade su na…

Read More